Gwamnatin tarayya ta yi kira ga Kungiyar Kwadago ta Ksa (NLC), da ta janye zanga-zangar da ta ke shirin yi a fadin kasar nan domin nuna goyon baya ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).
Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan yi, Chris Ngige ne, ya yi wannan roko a wani taro da shugabannin kungiyar NLC a ofishinsa a jiya Alhamis a Abuja.
- Larabawa Sun Yanke Kauna Da Tsarin Demokradiyyar Yammacin Duniya
- Cikin Watanni Uku An Haifi Yara Sama Da 27,000 A Kano
Idan za a iya tuna cewa, NLC ta yanke shawarar shiga zanga-zangar ne a fadin kasar ne a taronta na Majalisar Zartarwa, NEC, a watan Yuni.
kungiyar ta shirya gudanar da zanga-zangar ne a ranakun 26 da 27 ga watan Yuli, domin tabbatar da cewa dalibai sun koma makaranta da kuma goyon bayan ASUU da ke fafutukar neman ilimi mai inganci.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Olajide Oshundun, Ngige ya ce gwamnatin tarayya ta yi kokari matuka wajen ganin an shawo kan tabarbarewar harkokin jami’o’in, inda ta ce har yanzu ana ci gaba da kokarin.
Ya kuma tunatar da shugabannin NLC cewa ya shigar da su cikin sulhun bangarorin uku da ke gudana a ma’aikatarsa.
Ngige ya kara da cewa NLC na sane da kokarin gwamnati na ganin an shawo kan matsalar, don haka bai kamata ta gudanar da wani gangami ko zanga-zanga ba.
Ya ci gaba da cewa majalisar zartaswa ta tarayya (FEC), ta umarce shi da ya sanar da NLC din mummunar illar da za ta shafi tsaro idan ta gudanar da zanga-zangar da ta shirya yi.