A wasu jerin munanan al’amura da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun kashe aƙalla mutane 42 a wasu hare-hare daban-daban a ƙauyukan jihohin Zamfara da Katsina.
A ƙauyen Magarya da ke ƙaramar hukumar Zurmi ta Zamfara, mutane 12 ne suka mutu, ciki har da ƴansanda bakwai, yayin wani hari da wasu ƴan bindiga kusan 300 suka kai ranar Alhamis. Ƴan fashin dajin sun kuma raunata wasu da dama, sun ƙona gidaje biyu, da motoci sannan kuma suka sace dabbobi da dama.
- Dole Ne Waɗanda Suka Kashe Sojoji Su Fuskanci Hukunci — Minista
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Wasu Malaman Jami’a A Jihar Katsina
Kwamishinan ƴansandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu Dalijan, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya jaddada fushin ƴan bindigar kan nasarar da ƴansandan suka yi na daƙile ayyukansu tsawon shekaru biyu da suka gabata.
Mazauna yankin, waɗanda yanzu haka suka firgita da ƙarin hare-haren, sun tsere daga ƙauyen, inda suka nemi mafaka a Gusau da garuruwan da ke kusa.
Wannan dai shi ne karo na huɗu da aka kai wa Magarya hari, inda ukun farko suka faru kafin a tura jami’an tsaro.
A jihar Katsina wasu ƴan bindiga sun ƙaddamar da sabbin hare-hare a ƙauyuka da dama, inda suka kashe akalla mutane 30.
Hare-haren sun tilastawa mazauna garin tserewa zuwa garin Dutsinma da ƙauyen Turare domin tsira da rayukansu. Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta tabbatar da faruwar harin amma har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba.