Yayin da kasar Sin ke kara kaimin bunkasa samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, adadin iskar gas da aka yi amfani da ita a kasar cikin watanni 4 na farkon shekarar bana, ya karu da kaso kaso 11.9 bisa dari, idan an kwatanta da na makamancin lokaci na bara.
Alkaluman hukumar bunkasa ci gaba da aiwatar da sauye sauye ta kasar sun nuna cewa, adadin iskar gas din da aka yi amfani da ita tsakanin watan Janairu zuwa Afirilun bana, ta kai kyubik mita biliyan 143.73, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 11.9 bisa dari a shekara. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp