Yau rana ce da ake bikin Duanwu na gargajiyar kasar Sin, bikin da ke da tsawon tarihin fiye da shekaru 2000, wanda kuma ke kunshe da al’adun Sin masu zurfi.
A zamanin gargajiya na yake-yaken dauloli, wato sama da shekaru 300 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam (AS), jama’a a wancan lokaci su kan ci wani nau’in abinci mai suna “Zongzi”, wato dafaffiyar shinkafa mai yauki da aka kunsa cikin ganyen tsaure, a kan kuma aiwatar da sauran harkoki don tunawa da wani shahararren mawaki na daular Chu mai suna “Qu Yuan”,wanda ke matukar kishin kasarsa. Al’ummar Sinawa sun yi gadon wannan al’ada daga zuri’a zuwa zuri’a har zuwa yanzu.
A cikin dubban shekarun da suka gabata, Sinawa na yabawa Qu Yuan game da ruhinsa na kishin kasa da yadda ya bayar da muhimmanci ga al’umma. Suna tunawa da shi ta hanyar cin “Zongzi” da yin gasar tseren kwale-kwale da sauransu, kuma a halin yanzu, an yi gadon ruhi da tunaninsa tare kuma da hada su da zaman rayuwar jama’a ta zamani don kara yayata shi, har ya haskaka a duk fadin duniya. Hakan ya sa, hukumar UNESCO ta shigar da wannan biki a cikin jerin sunayen abubuwan tarihin duniya da ba na kayayyaki ba, wanda ya zama bikin gargajiya na farko daga kasar Sin da UNESCO ta shigar cikin jerin, wanda ya sa al’ummar Sinawa ke alfahari da al’adunsu. (Mai zane da rubutu: MINA)