A ƙalla ƴan kasuwa 5,000 ne za su rasa shagunansu waɗanda ke kasuwanci a kusa da babban masallacin Idi na Kano, biyo bayan sanarwar da hukumar tsare-tsare da raya birane ta jihar Kano, KNUPDA ta yi musu.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, Shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar, Yakubu Muhammad, ne ya bayyana haka a ranar Talata yayin wata ganawa da manema labarai.
- Kansila Ya Ɗauki Nauyin Karatun Ɗalibai 120 A Kano
- Boko Haram Sun Sace Fasinjoji A Kan Hanyar Maiduguri Zuwa Kano
Hukumar KNUPDA ta bayar da wa’adin sa’o’i 48 ga ‘yan kasuwa a masallacin da ke kan titin IBB a cikin birnin Kano da su bar gurin ko kuma su fuskanci fushin doka.
Malam Muhammad ya bayyana cewa shekaru 18 da suka gabata Marigayi Galadima na Kano, Tijjani Hashim ne ya raba musu wurin ta hannun Masarautar Kano.
“An ware wurin ne ga mambobinmu domin duba ayyukan laifuka daban-daban kamar satar waya da sauran ayyukan ɓata gari da ake tafkawa a wuraren,” inji shi.
Ya ce gwamnatocin da suka gabata a jihar sun ga ya dace a bar ‘yan kasuwar su ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankin.
“Muna da yawa a nan, galibi matasa ne, ta yaya za ku yi ƙoƙarin raba waɗannan mutane da kasuwancinsu, kun san hakan zai haifar da haɗari ga jihar,” in ji shi.
Malam Muhammad ya ce, “Har yanzu muna ƙoƙarin ganin mun shawo kan haƙiƙanin laifin da muka aikata wanda ya sa KNUPDA zata fatattake mu daga inda muke gudanar da sana’o’inmu na halal ba domin kula da iyalanmu.
“Mun goyi bayan wannan gwamnati. Mun zabe shi a lokacin zaben 2023. Mafi kyawun sakayyar da wannan gwamnati za ta yi mana bai wuce ta ba mu damar ci gaba da kasuwancinmu a Masallacin Idi,” in ji shi.
Da aka tuntubi wata majiya a KNUPDA da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da cewa hukumar ta umurci ‘yan kasuwar da su bar wurin saboda sun mamaye wurin ne ba bisa ka’ida ba.
“KNUPDA na ganin ‘yan kasuwar ba su nemi izini daga gare ta ba kafin su fara kasuwanci a can.” Inji majiyar.