A yau Laraba ne wani jirgin ƙasa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ya kauce daga titin Abuja zuwa Kaduna, lamarin da ya zama karo na uku a cikin sama da makonni biyu, daga ranar 26 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yunin 2024.
Wani ma’aikacin hukumar kula da jiragen ƙasa ta Najeriya NRC, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da taɓarɓarewar lamarin tare da amma ya bayyana ƙoƙarin da ake yi na gyara lamarin.
- Jirgin Ƙasan Kaduna Zuwa Kano Zai Fara Aiki Farkon 2025
- NRC Ta Dakatar Ma’aikacinta Kan Karbar Kudin Fasinja Ba Bisa Ka’ida Ba
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya bayyana cewa wani babban Manajan Darakta na cikin jirgin yayin da lamarin ya faru. Bugu da ƙari, wani mai amfani da shafin X mai suna Norbert Shialsuk ya ce sun yi sa’a sauka daga hanyar jirgin ya afku a lokacin da suka isa Abuja, domin da a daji ne da komai na iya faruwa.
Ya zuwa yanzu, hukumar ta NRC ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da karkacewar da layin jirgin yayi.