Hukumar Tarayyar Turai a ranar Laraba ta bayyana jerin harajin kariya da za ta dora kan shigo da motocin lantarki masu amfani da batura daga kasar Sin, lamarin da ya haifar da adawa da damuwa daga gwamnatoci da ’yan kasuwa a fadin Turai.
Ministan tattalin arzikin kasar Hungary Marton Nargy ya yi Allah wadai da matakin. Yana mai cewa kariyar ta wuce gona da iri. A cikin bayaninsa ya ce, “kakkaba takunkumin haraji da nufin ba da kariya ga cinikayya ba shi ne mafita ba,” kuma matakin da hukumar ta dauka za ta kasance rashin adalci da nuna wariya ga masana’antun kasar Sin, da kuma kawo cikas ga gasar kasuwanci, wadda ta kasance muhimmiya ga Tarayyar Turai.
- Xi Jinping: Sin Za Ta Ci Gaba Da Kasancewa Cikin Rukunin Kasashe Masu Tasowa
- Gazawar Fahimtar Juna, An Ɗage Shari’ar Yahaya Bello
Volker Wissing, ministan Tarayyar Jamus mai kula da harkokin dijital da sufuri, ya bayyana a dandalin sada zumunta na X cewa, harajin zai shafi kamfanonin Jamus da kayayyakin da suke fitarwa zuwa ketare, “Dole ne motoci su zama masu rahusa ta hanyar karin gasa, da bude kasuwanni da ingantaccen yanayi a cikin EU, ba ta hanyar rikice-rikice na cinikayya da kebenta kasuwa ba.”
Shugaban kamfanin BMW Oliver Zipse ya soki shirin hukumar da cewa “hanyar da ba ta dace ba.” Yana mai cewa hakan zai lalata kamfanoni da muradun Turai, “Ba da kariya ga cinikayya yana da hadarin haifar da sarkakiyar al’amari, zai haifar da yanayin dora haraji kan haraji wanda ka iya haifar da sabbin tsarin haraji, har ya kai ga kebance kasuwanni maimakon hadin gwiwa,” a cewarsa. (Mohammed Yahaya)