Duk da kiraye-kiraye da kasar Sin ta rika yi don gane da bukatar warware takaddamar cinikayya tsakaninta da kungiyar tarayyar Turai ta EU, hukumar gudanarwar kungiyar ta sanar da matakin kara harajin kaso 38.1 bisa dari, kan motoci masu amfani da lantarki kirar kasar Sin ko EVs da ake shigarwa kasashe mambobin kungiyar, matakin da ko shakka babu zai yi tarnaki ga kyakkyawar alakar raya tattalin arziki dake tsakanin Sin da EU.
Kafin sanar da matakin na EU dai, kungiyar ta yi zargin cewa kamfanonin kirar motoci samfurin EVs na kasar Sin na samun rangwame daga gwamnati, don haka EU ke ganin wajibi ne ta karawa sashen haraji domin cike gibin cinikayyar motocin.
- Xi Jinping: Sin Za Ta Ci Gaba Da Kasancewa Cikin Rukunin Kasashe Masu Tasowa
- Sojojin Nijeriya Sun Kashe Ƴan Bindigar Daji A Dajin Taraba, Sun Ƙwato Makamai Da Kayan Aiki
To sai dai masu fashin baki da dama na ganin wannan batu na kara haraji na da nasaba da siyasa, ba wai tsantsar harkar tattalin arziki ba ne. Hakan ne ma ya sanya, da yawa daga kamfanonin kirar motoci na Turai suka bayyana adawa da wannan anniya ta kara haraji kan motocin EVs kirar kasar Sin.
Kaza lika, a matsayinsu na manyan budaddun kasuwanni, kuma masu taka muhimmiyar rawa a fannin dunkulewar duniya, Sin da EU na da masana’antu, kuma suna rarraba hajojinsu zuwa sassan duniya daban daban, a wani yanayin dake hade da juna, ta yadda zai yi wuya a iya raba tsakanin hada-hadar da suka jima suna gudanarwa tare.
Ana iya ganin wannan alaka a sashen cinikayyar motoci tsakanin sassan biyu. Alal misali, motocin da ake kerawa a Turai na samun matukar karbuwa a kasuwannin Sin. Yayin da a daya hannun, kamfanonin kera motoci na Sin suka shafe tsawon shekaru suna zuba jari, da daga matsayin fasahohinsu na kirkire-kirkire, har suka kai matsayin shiga takara mai inganci a fannin samar da motoci samfurin EVs, wadanda kasuwarsu ke matukar habaka yanzu haka a Turai.
Don haka dai ya kamata bangaren EU ya yi karatun ta nutsu, ya yi watsi da matakai na kariyar cinikayya, domin aiwatar da hakan ba abun da zai haifar sai koma baya. Kuma wannan mataki da wasu tsirarun ’yan siyasar Turai ke yayatawa, zai jefa al’ummun kasashensu cikin mawuyacin halin tsadar hajoji a wannan fanni, da rage damar su ta more kyakkyawar rayuwa.
Har ila yau, matakin karin harajin zai iya nuna rashin tabbas game da manufar da EU ta ce tana kai, ta sauya akala zuwa ga samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da shawo kan kalubalen sauyin yanayi. Ya dace EU ta yi nazari sosai, ta sauya matsaya domin kaucewa “Haihuwar ‘Da Maras Ido”! (Saminu Alhassan)