Mahukunta a ma’aikatar sufurin jiragen kasa ta kasar Sin, sun ce tsakanin watan Janairu zuwa Mayun bana, sashen sufurin jiragen kasa na kasar ya yi jigilar fasinjoji biliyan 1.73, adadin da ya nuna karuwar kaso 20.2 bisa dari a shekara guda.
Alkaluman hukumar sun kuma nuna cewa, tsakanin wa’adin watanni 5 na farkon shekarar ta bana, a kullum a kalla jiragen dakon fasinja 10,463 ne suka yi zirga zirga, adadin da ya nuna karuwar kaso 12.7 bisa dari a shekara. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp