Rundunar sojan ƙasan Nijeriya ta gudanar da bikin yaye sabbin sojoji kashi na 86 da yawansu ya kai 5,937 a cibiyar horon soja da ke DEPO a Zariya a Jihar Kaduna.
Cikin jawabinsa yayin taron Babban Hafsan Sojoji Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya ce za a tura sojojin bakin daga domin yaƙi da ‘yan fashi da satar shanu da sauran ƙalubalen tsaro a ƙasar nan.
- Amurka Za Ta Aika Wa Ukraine Karin Makamai Masu Linzami
- An Kaddamar Da Ficewar Sojojin Amurka Daga Nijar A Hukumance
Ya jinjina wa cibiyar tare da jan hankalin sabbin kuratan da su zama jakadu na ƙwarai a duk inda suka samu kansu.
Bayan kammala faretin girmamwa an bayar da lambabin yabo ga hazikan sojojin da suka nuna bajinta a yayin da suke samun horon aikin sojin.
Daga cikin mayan baƙin da suka halarci bikin har da mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, da mai martaba sarkin Zazzau, Dakta Ahmad Nuhu Bamalli, da manyan jami’an gwamnati daga wurare daban-daban