Florence Morenike Saraki, mahaifiyar tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ta rasu tana da shekaru 89. Ta kasance matar shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu kuma ta rasu a ranar Talata.
Dakta Saraki, wanda ya kasance gwamnan jihar Kwara har sau biyu, ya tabbatar da rasuwarta a sahfin X, inda ya bayyana matuƙar baƙin ciki da miƙa wuya ga ikon Allah. Y ba da sanarwar a jiya 18 ga Yuni, 2024.
- Alhazan Abuja Da Kogi Sun Yaba Wa Ƙoƙarin NAHCON A Madina
- An Ceto Ragowar ÆŠaliban Jami’ar Da Aka Yi Garkuwa Da Su Jihar Kogi
Dakta Saraki ya nuna jin dadinsa da irin kauna, da addu’o’in da ya samu a wannan lokaci na juyayin mahaifiyar tasa.