Nijeriya ta koma matsayi na 38 cikin kasashen da suka fi iya kwallon kafa a duniya bayan wata kididdiga ta baya-bayan nan da hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar a ranar Alhamis.
Yanzu Super Eagles tana da maki 1498.93, wanda ya ragu daga maki 1520.27 da suke dashi a baya, hakan kuma babban nakasu ne ga hukumar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF).
- Sin Na Goyon Bayan Kokarin Kasashen Afrika Na Magance Matsaloli Ta Hanyar Da Suka Zaba
- Rikicin Ƴan daba Yayi Sanadin mutuwar mutum 1, Da Raunata 2 A Kano
A baya Nijeriya tana matsayi na 30, ta samu wannan koma bayan ne bayan ta yi rashin katabus a wasannin da ta buga bayan kammala gasar cin kofin Afrika, wanda ta kare a ta biyu bayan ta sha kashi a hannun masu masaukin baki da ci 2-1 a wasan karshe.
A wasannin da suka buga na baya-bayan nan, Super Eagles ta buga kunnen doki 1-1 da Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu, a birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom, kuma ta sha kashi a hannun Jamhuriyar Benin da ci 2-1 a wasan da suka buga a Ivory Coast.
A halin da ake ciki dai, Argentina ta ci gaba da zama ta farko a jerin kasashen, inda ta tabbatar da matsayinta na kan gaba a fagen kwallon kafa a duniya.