Wata uwa ‘yar kasar Zimbabwe da danta sun yi ikirarin cewa suna soyayya da juna kuma sun yanke shawarar su yi aure bisa la’akari da cewa mahaifiyar Betty Mbereko (daga Mwenezi a Masbingo) tana da ciki wata shida a yanzu kuma tana jiran haihuwar abin da ke cikinta wanda zai zama danta kuma jikanta.
Mbereko, mai shekaru 40, ta kasance bazawara tun shekaru 12 da suka gabata inda take zaune da danta mai shekaru 23 mai suna Farai Mbereko.
- Gwamnan Kano Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Kawo Karshen Fadan Daba A Kano
- Harajin Da EU Ta Sanyawa Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Kasar Sin, Ita Zai Yi Wa Illa
Ta tabbatar da cewa tana da ciki wata shida kuma ta yanke shawarar cewa zai fi kyau ta “aure” danta domin ba ta son auren ’yan’uwan mijinta da ya rasu, wadanda ta ce suna matukar kwadayin ganin sun aure ta.
Betty ta girgiza wata kotun akuye a makon da ya gabata lokacin da ta ce ta fara kaunar dan nata ne a matsayin wanda za ta iya aura tun shekaru uku da suka wuce. Ta ce bayan kashe makudan kudade ta tura Farai makaranta bayan rasuwar mijinta, don haka ta ji cewa tana da hakki a kan kudin da yake samu yanzu domin babu wata mace da ta cancanci hakan.
“Duba da cewa, ni kadai na yi ta fama da gwagwarmaya don in tura dana makaranta, ba wanda ya taimake ni. Yanzu ka ga dana yana aiki kuma don na ce zan aure shi sai ka zarge ni da aikata ba daidai ba?
“A bar ni kawai in ji dadin gumina da na barje,” ta fada wa kotun kauyen.
A nashi bangaren, dan nata, Farai ya ce shi kansa ya fi son ya aure mahaifiyarsa kuma zai biya ragowar bashin sadakin da mahaifinsa ya gadar wa a kakanninsa.
“Na san mahaifina ya rasu kafin ya gama biyan kudin sadaki kuma a shirye nake in biya,” in ji shi.
“Yana da kyau a bayyana abin da ke faruwa domin mutane su sani cewa ni ne na yi wa mahaifiyata ciki. Idan ba haka ba, za su tuhume ta da fasikanci.”
Sai dai kuma, Dagacin kauyen, Nathan Muputirwa ya ce: “Ba za mu kyale hakan ya faru a kauyenmu ba, domin hakika wannan mummunan al’amari ne). Idan da a zamanin baya suka yi hakan dole ne a zartar musu da hukuncin kisa amma a yau ba za mu iya ba saboda muna tsoron ‘yansanda.”
Ya gargade su da su gaggauta yanke wannan kudiri na auren junansu ko kuma su bar kauyen da zama.
Tuni dai majiyarmu ta bayyana cewa uwar da dan sun zabi su yi hijira daga kauyen inda suka koma wani wuri da ba a bayyana ba.
Majiya: One Africa