Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz, ya bai wa alhazai da suka kammala aikin Hajji kyautar Al-kur’anai ga kowane Alhaji da zai koma gida.
Kafar yada labarai ta Saudi Gazzet ce ta ruwaito cewa a ranar Asabar ma’aikatar harkokin addinin musulunci da da’awah ta ƙasar ta rabar da kimanin kofi 52,752 na Al-qur’ani mai girma ga alhazan da suka tashi a filin jirgin saman birnin Jedda na kasar Saudiyya.
Bayar da kyautar wata shaida ce ta girmamawa da sarkin ke yi wa dukkan alhazan da suka sauke farali a duk shekara.
Akalla mahajjata fiye da miliyan 1.8 ne daga ƙasashen duniya suka sauke farali a wannan shekarar ta 2024.
Alhazan da suka rabauta da kyautar sun nuna jin dadinsu kan kyautar karramawar da Sarki Salman ya yi musu a lokacin da suke bankwana da kasar ta Saudiyya.