Majalisar zartarwa ta amince da Dala Biliyan $1.442b da kimanin Naira Biliyan ₦2b ga hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA domin inganta ayyukanta.
Ministan Shari’a na ƙasa, Prince Lateef Fagbemi, SAN ne ya sanar da hakan bayan taron majalisar da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya jagoranta, za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen sayo kayan aiki da ababen hawa.
- Hajjin Bana: NDLEA Ta Kama Maniyyata Dauke da Hodar Iblis A Legas
- Babu Mai Faɗa Maka Matsalar Tsaro Daga Amurka Fiye Da Wanda Abin Ya Shafa – Radda
Kuɗaɗen da aka amince da kashe wa sun haɗa da Naira Biliyan ₦1.9b don siyan motocin Mikano Maxus E60 masu kama da CNG guda 33 domin inganta ayyukan hukumar ta NDLEA.
Bugu da ƙari, za a ware Dala Biliyan $1.442b don sayan makamai, da alburusai, da na’urorin yaƙi da turjiya don ayyukan yaƙi da muggan kwayoyi.
Hakazalika, za a kashe Naira miliyan ₦985m wajen sayen na’urorin ɗaukar hoto guda biyu don sanyawa a filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa a Abuja da Legas. Fagbemi ya jaddada mahimmancin waɗannan sayayyar don tallafawa ƙoƙarin NDLEA na yaƙi da fatauci da shan miyagun ƙwayoyi yadda ya kamata.