Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kai karar majalisar dokokin jihar kan zargin gwamnatisa da karkatar da Naira biliyan 432.
Majalisar ta yi zargin cewa ya yi amfani da Naira biliyan 432 ba bisa ka’ida ba a tsawon wa’adinsa na shekaru takwas, wanda ya hakan ya jefa jihar cikin kangin bashi.
- Gwamnatin Sakkwato Na Ci Gaba Da Shirin Tsige Sarkin Musulmi – MURIC
- Majalisar Dokokin Sakkwato Ta Gabatar Da Kudirin Rage Wa Sarkin Musulmi Iko
Lauyan El-Rufai, Abdulhakeem Mustapha, ya shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Laraba.
Lauyan ya kalubalanci rahoton majalisar da ya zargi El-Rufai da karkatar da dukiyar jama’ar jihar.
Kwamitin majalisar dokokin jihar, ya yi bincike game da wasu kudade, bashi da kwangiloli da El-Rufai ya bayar a lokacin mulkinsa.
Kakakin El-Rufai, Muyiwa Adekeye, ya ce har yanzu ba su samu rahoton ba amma za su yi martani da zarar sun samu rahoton.
Ya jaddada cewar gwamnatin El-Rufai, ta yi aiki bisa gaskiya, inda ya ce sun yi watsi da ikirarin majalisar dokokin.