Shugaban hukumar kula da harkokin siyasa da shari’a ta kwamitin kolin JKS, Chen Wenqing, ya gana da wata tawagar manyan alkalai daga kasashen Afrika, jiya Talata a birnin Beijing.
Yayin ganawar, Chen Wenqing, wanda kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya ce cikin shekarun baya-bayan nan, kasashen Sin da Afrika sun cimma matsaya kan batutuwa da dama da suka shafi raya hadin gwiwar manyan tsare-tsare a tsakaninsu da gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya da tsara shirin raya hadin gwiwarsu mai dogon zango.
- Yanzu-Yanzu: Dalibai 6 Sun Nutse A Kogin Kaduna
- Shugaba Xi Na Kasar Sin Ya Amsa Wasikar Da Mutanen Gundumar Jingning Suka Aika Masa
Ya ce a shirye kasar Sin take ta hada hannu da kasashen Afrika wajen aiwatar da matsayar da suka cimma da shugabanninsu, da zurfafa musayar ra’ayi game da dangantakarsu, musammam ingantaccen hadin gwiwa a fannin shari’a.
A nasu bangare, mambobin tawagar sun ce za su inganta musaya da koyo daga juna tsakanin Sin da Afrika, kan harkokin shari’a. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)