Majalisar dattawa ta kira wani zama na gaggawa domin duba yin wani sabon kasafin kuɗin ƙari akan na shekarar 2024 na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda zai kunshi kuɗin sayen sabon jirgin shugaban ƙasa. Wannan shawarar ta biyo bayan hutun da ƴan majalisar wakilai da majalisar dattawa suka fara a makon jiya, tare da shirin komawa ranar 2 ga watan Yuli, 2024.
Sanata Yemi Adaramodu, shugaban kwamitin majalisar dattijai kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, ya bayyana cewa majalisar za ta gudanar da zamanta ranar Alhamis domin tattauna batutuwa daban-daban da suka haɗa da kasafin kudi.
Ya yi nuni da cewa majalisar dattawan ta yanke shawarar komawa ne tun da farko domin samun ƙarin lokaci don tunkarar al’amuran ƙasa da na tsarin mulki.
- Samar Da Jami’ar Musulunci A Jihar Kaduna Alheri Ne – Bola Ige
- Za Mu Canza Salon Yaƙin Da Muke Yi Da Ƴan Bindiga a Nijeriya – Bola Tunibu
Wannan ya haɗa da ci gaba da sa ido kan kasafin kuɗi da magance batutuwan da suka shafi tsarin mulki da na zaɓe, da kuma kudurori kafinsu tafi hutun su na shekara daga baya a nan gaba.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta iƙirarin cewa Majalisar ta amince da sayen sabbin jiragen shugaban ƙasa, yana mai bayyana irin waɗannan rahotannin a matsayin son kawo ruɗani.
Sai dai kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaro da leƙen asiri ya ba shugaban kasa da mataimakinsa shawarar sayo sabbin jiragen sama saboda jiragen fadar shugaban ƙasa sun tsufa kuma zasu iya haifar matsala.
An kuma bayyana cewa fadar shugaban ƙasa ta sanya uku daga cikin waɗannan jiragen a kasuwa domin sayarwa.