Akwai wuraren ajiye kayan tarihi masu dama da miliyoyin musulmi ke turuwar zuwa domin ilimantar da kasu a garin Al-Makkatu Mukarramah da Madinah Al-Munawara a duk shekara.
Bayan kammala ayyukan ibada na Umara ko Hajji tare da gudanar da dawafi da sa’ayi, alhazai kan kuma kosa su ziyarci wasu wurare masu muhimmanci a tarihin addinin musulunci.
- Kamfanin Kera Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Sin Ya Shiga Kasuwar Kenya
- Summer Davos: An Tattauna “Sababbin Damammaki A Kasar Sin”
Garuruwan biyu nada tarihin da ya wuce dubban shekaru, sun kuma danfaru da tarihin addnin musuluncin ne gaba daya, za kuma su ga yadda wasu al’adu da gine-ginen garuruwan suka canza a tsawon shekarun da suka wuce.
Wuri na farko da ya kamata Alhaji ya ziyarta shi ne unguwar da ake kira da ‘Unguwar Al’adu ta Hira’.
Domin fahimtar tarihi da muhimmancin wadannan garuruwan, dole mai ziyara ya yi nazarin muhimmancin su ga addinin musulunci, ana shawartar Alhazai su samu ziyartar wurare kamar Jannat Ul Mua’lla, Kogon Hira a kan dutsen ‘Jabal Al-Nour’, Dutsen Arafat da masallacin Ayesha.
Haka kuma a kusa da masallacin Haram akwai wuri mai muhimmanci da aka fi sani da Hudaibiyah, wurin da Manzo (SAW) ya sanya hannu a yarjejeniyar Hudaibiyah. Domin taskace tarihi da muhimmancin wurin a yanzu an gina masallaci a daidai wurin.
A shekarar 809, lokacin da aka fuskanci tsananin rashin ruwa a garin Makkah, Sarauniya Zubaida, matar Kalipha Harun Rashid, ta tafi aikin hajji, inda ta lura da wahalar da al’umma ke fama na rashin ruwa, a kan haka ta bayar da umarnin gina tafkin da aka fi sani da ‘Zubaida Canal’.
Yanzu shekaru dubbai ke nan alhazai na ci gaba da amfana da ruwan da ke fitowa daga tafkin.
Sai kuma dutsen Abu Kubais, inda mu’ujizar nan na wata ya faru, zai kuma ci gaba da kasancewa wani abin tunatarwa game da mu’ijizozin addinin musulunci.
Wani wurin da ya kamata alhaji ya ziyarta shi ne gidan tarihi na “Assalaamu Aleyka Ayyuhan Nabiyyu” a nan masu ziyara za su gani a bayyane tarihin rayuwar Annabi Muhammadu (SAW), ta hanyar kayayyakin da ya yi amfani da su a lokacin yana raye za su samu damar fahimmatar rayuwarsa da na kakanninsa, matansa, yaransa da sauran abubuwan da suka shafi gwagwarmayarsa ta tabbatar da addini. An kafa wannan gidan tarihi ne da hadin gwiwar malamai da masana fiye da 150 domin tabbatar da inganci da sahihancin abubuwan da aka samar a gidan.
Wani mai suna Ahmed Khanya ya bayyana cewa, shekararsa 15 yana aikin zagayawa da Alhazai wurare masu tsarki a garuwar Makkah da Madina.
“A kodayaushe Alhazai na jin dadin ziyartar wuraren da ke tattare da tarihin Manzon Tsira Muhammad Dan Abdullahi wanda hakan ke taimaka musu samun cikakkiyar fahimtar tarin addinin musulunci.”
Wasu wuraren sun kuma hada da kogon Hira a nan ne Manzon Allah (SAW) da Sahabinsa Abubakar suka boye a lokacin da Kuraishawa suka kai musu hari a yayin da suke hijira zuwa Madinah.
A garin Madinah, wanda ita ce ta biyu a daraja, musulmi shaukin ziyartar wuraren tarihi a garin da suka hada da, Masjid Al-Kiblatain, Masjid Abu Bakr, Masjid Al-Ahzab haka kuma akwai Masjid Al-Ghamamah duk da kankancinsa yana da muhimmanci don neman albarka a garin Madinah. Akwai kuma makabartar Baki’a da filin da aka tafka yakin Uhud.
Haka kuma akwai wuraren da aka yi wasu yake-yake masu matukar tarihi a addnini musulunci kamar yakin Khandak da aka yi a shekara ta 624 bayan hijira, a halin yanzu an gina babban masallaci a daidai wurin da aka yi yakin a tsakanin Musulman Madinah da Mushirikan Makkah.
Akwai kuma gonar Sayiddina Salman Farsi a Madinah inda tarihi ya nuna cewa, Manzon Allah (SAW) ya shuka dabino fiye da 300 domin ya ‘yantar da Salman Farsi daga bauta, daga nan kuma sai masallacin Kuba.
Ga wanda ya samu ikon zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da ibadar Umara ko aikin Hajji ya kamata ya nemi a kai shi ziyara wadanna wuraren domin suna kara wa mutum Imani da fahimtar addninin musulunci, zai kuma fahimci irin canje-canje da aka samu a tsawon shekarun da suka wuce.
Yadda Aka Yi Dawafi Da Kananan Motoci A Hajjin Bana
Hukumar kula da harkokin masallaci mai alfarma da masallacin Manzo (SAW) ta kaddamar da yin dawafi ta hanyar amfani da wasu kananann motoci domin amfani da Alhazawa masi bukata ta musamman da kuma attajirai.
An jibge motocin ne a kofar shiga ta ‘Ajyad Escalators’ da ‘King Abdulaziz Gate Elebators’ da kuma ‘Umrah Gate Elebators’ ta yadda masu bukata za su gan su ba tare da wani wahala ba.
Motocin suna aiki a kullum na tsawon awa 12, daga karfe 4 na yamma zuwa karfe 4 na asuba ga duk wanda yake bukata.
Farashin hawa motar ya fara ne daga Riyal 25, ga duk mai bukatar yin dawafi ba tare da fuskantar cunkoso ba, kuma a cikin dan kankanin lokaci. Ana iya samun tikitin hawa motar a harabar Masallacin.
A wannan shekarar an yi amfani ne da kananan motoci 50 inda kowanne ke daukar mutum goma.
Saboda yawan al’umma da kuma irin cunkoson da ake fuskanta yayin gudanar da ibada, hukumomin kasar Saudiya na ci gaba da kirkiro da hanyoyin saukaka yadda ake gudanar da wasu ayyukan ibada yayin aikin hajji.