Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makokin kwanaki uku bayan rasuwar sojojinta 20 da farar hula daya lokacin wani harin ta’addanci da ya rutsa da su a Kauyen Tassia na yankin Tilabery.
Lamarin ya faru ne a misalin karfe 10 na safiya a Kauyen Tassia Kudu da Band-jo dake karkarar Tera a Jihar Tilabery inda wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki kan dakarun gwamnati, in ji sanarwar ma’aikatar tsaro wacce ta kara da cewa wasu sojoji tara sun jikkata sannan an lalata motoci biyu yayin da askarawan gwamnatin suka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama tare da lalata masu ab-aben hawa.
- Lamarin Fanshon Tsofaffin Shugabanni A Nijeriya
- Shugaban Bankin Duniya Ya Yi Tsokaci Kan Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin
Jama’ar kasa na nuna juyayi dangane da yadda matsalar tsaro ke haddasa asa-rar rayukan jami’an tsaro da farar hula duk da matakan da hukumomi ke cewa suna dauka.
Gundumar Tera da ke matsayin yankin da Nijar ke iyaka da Burkina Faso na daga cikin wuraren da ‘yan ta’adda suka zafafa kai hare-hare a ‘yan watannin nan lamarin da ya tilasta wa mutane da dama neman mafaka .
Wani masani akan sha’anin tsaro Abass Moumouni na fassara lalacewar ya-nayin da karancin matakan hadin gwiwa saboda haka ya shawarci kasashen kawancen AES su gaggauta zartar da ayyukan rundunar da suka sanar cewa sun samar a watannin baya,
Jamhuriyar Nijar da ke kewaye da kasashen da ke fama da ayyukan kungiyoyi masu ikirarin jihadi na fuskantar hare-haren ta’addanci a yankunanta da dama musamman Jihar Tilabery dake iyaka da Burkina Faso da Mali.
Hakan ya sa sojojin kasar kifar da gwamnatin farar hula a watan Yulin 2023, haka kuma sabbin hukumomin sun kori sojojin kasashen Yammaci saboda zarginsu da rashin yin wani tabbas a yunkurin daidaita al’amura tare da maye gurabensu da dakarun Rasha masu aikin horo da nufin samo bakin zare, sai dai da alama har yanzu da sauran rina a kaba.