Wani jirgin sama mai saukar ungulu na Sojojin Saman Nijeriya, ya yi hatsari da sanyin safiyar yau Litinin a kauyen Tami, da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na safe bayan da jirgin ya fuskanci matsaloli wanda ya yi sanadiyar hadarin, tare da haifar da fargaba tsakanin mazauna kauyen.
- Ana Zargin Tsohon Shugaban Nijar Issoufou Da Yin Sama Da Faɗi Da Kuɗin Sayen Jirgin Sama
- An Gano Yadda Ake Amfani Da Jiragen Sama Masu Zaman Kansu Wajen Haramtacciyar Harƙyalla
Shaidun gani da ido a kauyen tuni sun bayyana farin cikinsu sakamakon rashin samun rasa rayuka da aka yi baya gano matukin jirgin daga cikin tarkacen jirgin tare da ko ƙwarzane ba.
Bayanai sun tabbatar da cewa tawagar jami’an soji daga rundunar sojin sama ta Nijeriya sun isa wurin da abun ya faru cikin gaggawa domin tabbatar da tsaron yankin tare da gudanar da bincike, inda su ka killace wurin da hadarin ya afku domin hana shiga ba tare da izini ba.
Jami’an sun kuma fara bincike domin gano musabbabin hatsarin, wanda kawo yanzu ba a iya gano ko mai ya jayo ba.