Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana kyakkyawar fatansa ga tawagar mu’amalar matasan Amurka da Sin wadda ke ziyara a nan kasar Sin a jiya Litinin.
Xi ya nuna cewa, makomar huldar kasashen biyu na dogaro da al’umomminsu, musamman ma matasan kasashen biyu. Yana mai fatan matasan Amurka za su kara fahimta da yarda da kasar Sin a ziyararsu a wannan karo, tare da sada zumunta da takwarorinsu a Sin, inda za su kafa wata gada mai kyau na kara fahimtar al’umommmin kasashen biyu, da ma taka rawar gani wajen karfafa zumuncinsu.
Kungiyar sada zumunta da kasashen ketare ta gayyato kuma ta tarbi wannan tawaga dauke da dalibai da malamai 190 daga makarantan midil 14 daga jihohi 7 na Amurka. (Amina Xu)