Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Tobi Amusan murnar lashe gasar tseren mita 100 na mata a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya 2022.
Shugaban kasar a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya fitar a ranar Litinin, ya kuma jinjinawa fitacciyar ‘yar wasan tseren gudun, wacce ta kafa sabon tarihin duniya a matakin wasan kusa da na karshe na gasar wasannin motsa jiki kuma ta zama ‘yar Nijeriya ta farko da ta taba lashe gasar cin zinariyar ta duniyan.
Shugaba Buhari ya bi sahun miliyoyin ‘yan Nijeriya wajen taya Amusan murnar wannan nasarar; ‘yar tseren, ta taba lashe gasar tsere ta Afrika sau biyu, wadda a cikin daren jiya ta baiwa duniyar wasanni mamaki da bajintar da ta taka.
Shugaban ya gode mata bisa sake sanya taken kasar Nijeriya sake Bayyana a dandalin kasa da kasa, wanda ya sanya al’ummar kasar Nijeriya cikin nishadi da hawayen murna da nasara.