Wani sabon rikici da ya barke ya yi sanadin mutuwar akalla mutane biyu tare da kone gidaje uku a wani sabon rikici tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa.
Rahotanni daga yankin sun ce bayan rashin fahimtar da aka samu tsakanin makiyaya da manoma, sun gayyaci ‘yan uwansu daga Jihar Katsina da ‘yan bindiga suka addabi yankin, inda suka fara lalata gonaki a kauyukan Safa da Gauraki.
- An Watsa Shirin “Bayanan Magabata Da Xi Jinping Yake So” Ta Kafofin Yada Labaran Kazakhstan
- A Tsarin Mulki, Sarkin Musulmi Ba Shi Da Ikon Naɗa Wani – Gwamnatin Sokoto
Rahotanni sun ce manoman sun bijire game da lamarin, inda abun ya rikide zuwa rikici tsakanin makiyayan da manoman.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Lawan Shi’isu Adam, ya bayyana cewa an kama wasu ’yan asalin yankin biyar da ake zargin sun gayyaci mutanen don tayar da zaune tsaye yayin da wasu shanu 15 na makiyayan suka bar su amma ‘yansanda sun kamo su.