- An Ce Mun Ce Alhali Ba Mu Ce Ba A Rahoton Majalisar
- A Tarihin Kaduna Ba A Taba Samun Kundin Mika Mulki Irin Na El-Rufai Ba
- Masu Kitsa Rikicin Siyasar Sun Boye Fuskokinsu
Tsohon kwamishina a gwamnatin Malam Nasiru el-Rufai, ALHAJI JAFARU SANI, da aka dama da shi har tsawon shekaru takwas shi ne wanda ya jagoranci kwamitin rubuta kundin bayanin mika mulki ga gwamnatin Malam Uba Sani bayan lashe zaben 2023. A wata zantawar da ya yi da wakilinmu a Kaduna, SHEHU YAHAYA, tsohon kwamishinan ya bayyana cewa suna bukatar kwamitin da ya koma baya ya dauko kundin bayanin mika mulkin da el-Rufai ya rubuta ya bai wa gwamnatin Uba Sani. A cewarsa, wannan ne ya kamata ya zama musu madogara kan bashin da aka ce tsohuwar gwamnatin ta ciwo da sauran abubuwan da suka shafi Jihar Kaduna. Kazalika, ya ce duk da rikata-rikitar da ake ciki, kofar el-Rufai a bude take domin yin sulhu kan matsalar. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance kamar haka:
Bari mu ji, wace rawa ka taka a gwamnatin el-Rufa’i a Jihar Kaduna?
Na rike ma’aikatu guda hudu a matsayin kwamishina a gwamnatin Malam Nasiru el-Rufai. Na rike ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu har sau biyu daga watan Fabrairu 2017 har zuwa Fabrairu 2018. Daga nan na tafi ma’aikatar kimiyya da fasaha. Bayan an yi zaben 2019, na kara dawowa ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu, daga nan na dawo ma’aikatar muhallai har lokacin da muka gama gwamnatin.
Da ku aka kafa gwamnatin Sanata Uba Sani a 2023, sai gashi kuma majalisar dokikin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin wucin gadi domin ya binciki badakalar bashi da tsohuwar gwamnatinku ta ciwo. Shin ya kuka ji da kuka samu labarin wannan rahoto?
Ko da muka ji wannan labarin, mu ba mu damu da kafa wannan kwamiti ba, saboda majalisa tana da dama ta yi abin da ya kamata. Tun da sun yi rantsuwa za su yi wa al’umma aiki tsakaninsu da Allah. Duk abin da suka yi indai sun san sun yi bisa gaskiya ai wannan ba wata matsala ba ce.
Ita gwamnati tana da daman ta yi abin da ya kamata wajen bankado wasu abubuwan da take ganin ya kamata ko kuma take ganin an yi ba daidai ba. Saboda haka, fito da wannan rahoto ba mu dauke shi da wata matsala ba ko kadan.
A cikin rahoton, ana zargin gwamnatinku da karkatar da biliyoyin naira da kuma karbar tarin Bashi. Shin ina gaskiyar wannan batu?
Toh! A nan ma akwai abin dubawa. Abu na farko dai shi ne, lokacin da Malam Nasiru el-Rufai zai bar gwamnati, ai ya yi jawabin mika mulki ga sabon gwamna, ya yi bayanin kan duk basussukan da ake bin gwamnatin Jihar Kaduna da kuma ayyukan da aka yi wadanda suke ba a biya ba. Da kuma hanyoyin da kudaden za su shigo wa sabuwar gwamnatin. Akwai basussuka daga gwamnatin tarayya wadanda kudin sun nuna karba kawai za a yi duka el-Rufai ya fitar da su a cikin jaddawalin mika gwamnati.
Kasan shi mulki kowa akwai yadda yake kallonsa. Akwai wanda ya kware ya kai matsayin darakta ko babban sakatare ko kuma ya yi aiki a ma’aikata mai zaman kanta, idan ka kalli yadda zai kama madafar aiki akwai bambanci da wanda bai taba yin aiki ba.
Akwai bayanai da kowacce ma’aikata ta hada na mika wa gwamnati, wanda haka yake sa ake kafa kwamitin karba da mika gwamnati. Wanda idan sabon gwamna ya zauna, sai a fara kiran manyan jami’an gwamnati suna kara bin kadin wannan rubutu da suka yi, saboda a kowacce ma’aikata akwai kwamishina da babban sakatare. Shi kwamishina dan siyasa ne wanda ba dole ba ne ya zama ya goge a cikin harkar gwamnati ba, amma kuma shi babban sakatare ma’aikacin gwamnati ne wanda da ya safe shekara 20 yana aikin gwamnati kafin zama babban sakatare. To ka ga akwai horuwa na sanin aiki tare da shi ko da kwamishina ya tafiya, gwamna zai iya sa sababbin kwamitin tuntuba ya kara bin wannan kundin bayanin da aka ba shi. Wanda wadannan manyan jami’an gwamnati duk suna ciki kuma ba za su yi karya ba, daman ai suna cikin kwamitin duk inda aka kwana aka tashi duk za su fadi.
Saboda haka idan aka bi wannan ka ga ka samu bayanan da aka nema. Amma a tsarin Kaduna ba a samu haka ba, saboda an kai lokaci da ake cigiya wai ina gwamnan yake ba ya Kaduna kullum yana Abuja, duk abin da ake nema sai a bi shi Abuja bai zo ya zauna ba an fahimci aikin ba ballantana a ce ga inda aka samu matsala a gyara ba.
Tun daga shekarar 1999 da aka fara gwamnatin siyasa, kowacce gwamnati za ta shigo tana shigowa ta tarar da basukan da ake bi da kuma ayyukan da aka fara da inda aka tsaya, wanne dan kwangila ne aka biya da wanda ba a biya ba. Wasu jihohin ma za ka tarar gwamna ya karbi gwamnati ma’aikata suna bin bashin albashi na wata takwas har fiye da haka kuma ga na ‘yan fansho. Irin wannan idan gwamna ya zo sai ya kalli kudirorinsa da ya yi yakin neman zabe da su da wanda ya tarar a kasa, sai ya daidaita su domin amfanar da al’ummar.
A 2015, lokacin da gwamnatin Malam Nasiru el-Rufai ta zo, ta tarar da irin wadannan matsala. Ashe ka ga ka shigo gwamnati ka tarar da abu ba irin yadda kake nufi ba, ba yau ne aka fara ba, sai dai dabarun yadda za ka tunkari wannan matsalar shi ne yake bambanta daidai da sanin aikinka.
Kun gurfana a gaban wannan kwamiti na majalisar dokokin jihar, kuma kun amsa tambayoyi kamar yadda kwamitin ya ce. Shin Ana iya cewa kun gamsu da sakamakon rahoton kwamitin kenan?
Gaskiya ba mu gamsu da sakamakon rahoton kwamitin ba. Lokacin da aka fara jita-jita majalisa za ta yi binciki tsohuwar gwamnati, sai muka ce bari mu tsaya mu ji abin da zai faru. Daga baya, sai muka ga ashe abin da gaske ne. Sai muka ce lokaci ya yi da za a ba mu dama mu yi wa mutane bayanin abin da suka sani, watakila suka manta. A tarihin Kaduna ba a taba samun kundin barin mika gwamnati gamsasshe irin wanda el-Rufai ya rubuta ya bai wa gwamnatin Uba Sani ba.
Amma duk da haka sai suka nuna ba su san abin da ake ciki ba, sai muka ce tun da haka ne, gashi majalisa sun kira mu to za mu samu damar fede biri har wutsiya domin mutanan Jihar Kaduna su san me ake ciki, su kuma fahimci ina aka kwana da inda aka tashi da inda matsalar take.
Sai muka yi roko cewa idan jami’anmu za su tafiya majalisar, muna son a ba da dama a tara mutane da gidajen talabijin da sauran ‘yan jaridu a yi abin a bayyane, saboda duk maganar da za a yi mutane su san abin da ake ciki. Amma majalisa ba ta amince da hakan ba, saboda haka tun tashin farko muka ce ba a yi mana adalci ba.
Duk da hakan sai muka ci gaba da zuwa zauren majalisa, kuma kowa ya shiga ya ba da bayaninsa ya fito cikin annashuwa da murna, saboda duk tambayoyin da ka yi musu sun amsa wadanda ake bukatar takardu sun bayar.
Muna zaune muna jira mu ga rahoto ya fito, kwatsam sai muka ji wani abu daban, sai muka yi mamaki, saboda an yi wani rubuta wai an ce kai ka ce kuma ba kai ka ce ba. Da muka kalli rahoton, sai muka ga rahoton ya saba da yadda aka rubuta shi, saboda majalisa ta kira tsoffin shugabanninta na takwas da na tara, Aminu Abdullahi Shagali da Yusuf Ibrahim Zailani duk tambayoyin da aka yi musu suka ba da amsa za a rubuta a kasa. Amma da kwamishinoni suka zo sai aka yi watsi da wannan tsarin na a yi maka tambaya idan ka ba da amsa a rubuta a kasa.
Tun daga nan sai aka nuna cewa akwai wani wurin da ake so a karasa, idan kuwa kana min tambaya ina baka amsa zai yi wuya ka ari bakina ka ci min albasa. Sun nuna su ne suke da mulki, sai suka fito da wannan rahoto da suka ce gwamnatin Malam Nasiru el-Rufai ta ci bashi. Mun kawo musu bayani kan basussuka guda biyar da gwamnatin ta amso kuma muka zayyano musu daya bayan daya.
A rahotonsu, sun ce akwai dala miliyan 430, na ma’aikatar muhalli da na shugabanta, wanda da ni aka yi ta kai komo kan bashin kuma na san dala miliyan biyu muka karbi bashi. Kuma wannan dala miliyan biyu mun rubuta ta a cikin kundin bayanin mika mulki wanda muka bar wa gwamnatin Uba Sani.
Idan kuma muka dauki bangaren ayyuka da majalisar ta yi magana a kai, abin da ya ba mu mamaki, sai suka dauko ayyuka guda 14 zuwa 15 aka shigo da su a cikin rahoton, suka ce yadda aka ba da wadannan ayyuka ba a bi doka ba, an saba wa dokar bayar da kwangila ta Jihar Kaduna. Wanda sun manta ita dokar shi el-Rufai ne ya kafa ta kuma ya mika wa majalisar suka mayar da ita doka. Amma rahoton ya kasa fito da yadda aka saba wa dokar, saboda ita dokar ta ba da hanyoyi da yawa da za a bi a bayar da kwangila, duk wanda yake zama a Kaduna ya san tsohuwar gwamnatin ta yi ayyuka manya sama da guda 200.
Sun dauko wani Abu da suka gani a ofishin babban akanta na Jihar Kaduna da ma’aikatar kudin da hukumar tara kudaden haraji sun ce an yi ba daidai ba. Kuma wannan rahoton da suka ce sun gani wani rahoto ne na wani kamfanin bincike mai suna ‘Deloyed’, wanda gwamnatin el-Rufai ta kaddamar da binciken ta biya kamfanin kudinsu, inda aka yi mata binciken taskar Jihar Kaduna tun daga shekarar 1999 zuwa 2019.
Daya daga cikin abin da duniya ta dauka a nata fadi shi ne, akwai naira biliyan daya da miliyan dari hudu da aka ce tsohuwar gwamnatin ta ba wani kamfanin zirga- zirga na ‘MISHA Trabel’, aka yi ta ihu aka ce ka ga barayi sun batar da kudin domin tafiye-tafiyensu zuwa kasashen waje. Bari na fayyace musu ma’anar MISHIA, ba ana nufin kamfanin zirga-zirga ba ne, ma’anarta shi ne, (MINISTRY OF INTERNAL SECURITY AND HOME AFFAIRS), wanda wani lokaci kwamishinan ma’aikatar muna kiransa ‘MISHA’, mu da sun tambaye mu za mu ce musu MISHA ana nufin ma’aikata ce ba kamfanin zirga-zirga jirage ba ne, saboda ta yaya za mu hau jirgin na biliyan daya da wani abu, kuma su a cikin rahoton nasu sun ce sun yi amfani da takardun bankuna ne suka zakulo abubuwansu. Amma kuma ba su bayyana takardun bankin ba.
To, ko ku kuna da naku alkaluman bashin da kuka dogara kansu?
Kamar yadda na fadi maka ne, mu muna kan matsayarmu na kundin bayanin mika mulki da tsohuwar gwamnatin el-Rufai ta rubuta ta ba sabuwar gwamnatin Uba Sani, shi ne zai tabbatar da gaskiyar abin da gwamnatin ta yi, saboda duk bayanan da suka yi na basussukan Jihar Kaduna ba haka suke ba, kuma idan ana batun ayyukan ne tun da aka yi Jihar Kaduna ba a taba samun gwamnatin da ta kwankwatsa aiki irin na gwamnatin el-Rufai ba. A tsarin gwamnati, dole sai ta tafi ta bar bashi.
Akwai wani jaddawalin da aka fito da shi na basuka na cikin gida na gwamnoni 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja a wannan shekarar ta 2024, Jihar Kaduna ita ma ta kara dibar bashin cikin gida. Shi cin bashi a gwamnatance ba wani abu ba ne, amma me ka yi da bashin da ka karbo shi ne abun magana.
Yanzu idan ka dauki hanyoyin da el-Rufai y ayi a cikin garin Kaduna da Zariya da Kafanchan da a ce an yi su tun a baya da yanzu wani abun aka yi a wani bangaren, saboda masu saka hannun jari suna so su ga inda za su saka hannun jari ne inda akwai irin wadannan ayyukan irin su hanyoyi masu kyau da wutar lantarki da sauransu.
Shi ya sa jihohin Yarbawa suka fi mu samun masu zuba hannun jari daga kasashen waje fiye da arewa. A Jihar Kaduna karkashin el-Rufai kwalliya ta biya kudin sabulu, saboda akwai kyaututtuka da gwamnatin ta samu sau uku a jere na samar da kyakyyawar yanayi na zuba hannun jari da yin kasuwanci.
Mu har yanzu ba mu dauki wannan abu da wata matsala ba, idan suna so, su zo mu zauna a gyara su ba mu dama mu horas da su kyauta ta hanyar bayar da kasidu domin a yi abin da ya kamata, saboda ba mu da wata jiha da ta wuce Jihar Kaduna. Shi Malam Nasiru el-Rufai har yanzu kofarsa a bude take wajen sulhu ko kuma yi musu gyara kan abin da ba su sani ba. Wanda haka ya kamata su yi tun farko ba kafa kwamiti ba.
Akwai Masu hasashen cewa wannan rikita-rikita kamar ana yi ne domin ya dusashe siyasar Malam Nasiru el-Rufai a 2027, me za ka ce?
Toh! Idan ka ce a’a ba haka ba ne, sai kuma ka ga wasu abubuwan sun bullo maka da suke tabbatar da hakan. Koma su wane ne suke yi sun boye fuskokinsu, amma a cikin gari da kauyuka wannan magana fa ta yi karfi sosai cewa wannan rigima ba cikin Jihar Kaduna ba ne ana hasashen daga wani wurin ne aka kawo ta. Kuma aka yi rashin sa’a wadanda suke kan mulki suka karbe ta. Amma da ba su amsa ba, da hakan ba za ta faru ba, saboda su sun san me ake ciki.
Kuma Gwamna Uba Sani shi ma jami’i ne mai fada a ji na tsohuwar gwamnatin Malam Nasiru el-Rufai. Ya san duk abubuwan da aka yi, domin da shi ake zaman majalisar zartaswa ta jihar. Ya san shigar komai, ya san fitar komai, saboda yana daya daga cikin mutanan da ake jin numfashinsu a waccan lokacin. Hausawa sun ce, “Ranar wanka ba a boyen cibi.”