Layukan sadarwa na 5G sun kai ga sama da kaso 90 bisa dari na kauyukan kasar Sin, bayan da fasahar ta 5G ta kai ga daukacin birane da garuruwan kasar.
Alkaluma daga ma’aikatar raya masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar sun tabbatar da cewa, Sin ta kafa tsarin fasahar sadarwa da watsa bayanai, wanda ke sahun gaba a duniya, mai kunshe da tashoshin 5G miliyan 3.84, adadin da ya kai kaso sama da 60 bisa dari, cikin jimillar wadanda ake da su a fadin duniya baki daya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)