Majalisar Wakilai ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar Samoa mai cike da cece-kuce.
Wannan shawarar ta biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa mai muhimmancin ga Æ™asa da ‘yan majalisar 88 suka shigar zauren majalisar a yau Talata.
- ‘Yansanda Sun Tura Mutumin Da Ya So Kashe Kansa Zuwa Gidan Mahaukata
- Tinubu Ya Taya Sheikh Dahiru Bauchi Murnar Cika Shekaru 100
Kudirin wanda dan majalisar wakilai, Aliyu Sani Madaki, na Jihar Kano, ya gabatar ya nuna damuwa kan wasu sharudan da ke cikin yarjejeniyar musamman wadanda suka shafi auren jinsi, wanda ya bayyana sashen a matsayin barazana da za ta iya gurgunta tarbiyyar al’ummar ƙasar nan.
Yarjejeniyar Samoa da gwamnatin tarayya ta sanya wa hannu da kungiyar Tarayyar Turai (EU), ta haifar da cece-kuce, inda mutane da yawa ke ganin ta amince da ‘yancin ‘yan madigo da luwadi wanda ya saba wa dokokin Nijeriya.
Tun da farko dai Ministan Kasafin Kudi da Tattalin Arziki Atiku Bagudu, da takwaransa na Yaɗa Labarai Mohammed Idris, sun tabbatar da cewa Nijeriya ba za ta shiga wata yarjejeniya da ta ci karo da ƙudin tsarin mulki ko addinai da al’adu ba, inda ya ƙara da cewa yarjejeniyar na da nufin bunkasa samar da abinci da tattalin arzikin da sauran muhimman batutuwa ne kawai.
Nijeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Samoa a ranar 28 ga watan Yuni, 2024, amma sai a makon da ya gabata bayananta suka iso kunnen jama’a.