Shugaba Bola Tinubu ya taya fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi murnar cika shekaru 100 a duniya.
Tinubu, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya sanar a ranar Talata, ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin mutum mai girma wanda ya bayar da gudummawa sosai ga addinin Musulunci.
- Â An Haramta Yi Wa Mata Kaciya A Gambiya
- Rikicin Masarautar Kano: Tinubu Da Sanusi II Suna Da Alaka Mai Karfi – Fadar Shugaban Kasa
Ya gode wa shugaban Tijjaniyyar bisa sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimi da kuma kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya.
“A wannan muhimmin lokaci, shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya kara wa Sheikh koshin lafiya da daraja,” in ji Ngelale.