A yau Talata, aka gudanar da taron dandalin hadin gwiwar gwamnatocin kananan hukumomin Sin da Afrika karo na biyar a birnin Guangzhou, wanda Liu Guozhong, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS kuma mataimakin firaministan kasar, ya halarta tare da gabatar da jawabi.
Liu Guozhong, ya ce a duniyar yau dake fama da rikice rikice, kana sauye-sauye ke karuwa, Sin da Afrika na bukatar karfafa hadin kai da hadin gwiwa fiye da kowanne lokaci. Ya ce dole ne gwamnatocin kananan hukumomi su hada hannu domin samun ci gaba da wadata na bai daya.
- ‘Yan Majalisu Sun Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Aiwatar Da Yarjejeniyar Samoa
- Xi Jinping Ya Gana Da Firaministan Hungary
Liu Guozhong ya kuma jaddada cewa, Sin na kokarin zamanintar da kanta, don gina kasa mai karfi da farfado da al’ummar kasar, kuma a shirye take ta samar da sabbin damarmaki ga kasashen Afrika daga sabon ci gabanta.
Kimanin mutane 350 ne suka halarci taron, ciki har da ‘yan siyasa daga kasashen Afrika da shugabannin gwamnatocin kananan hukumomi da hukumomi masu ruwa na kasashen Sin da Afrika. (Fa’iza Mustapha)