Shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ya ce, kasar Sin muhimmiyar abokiyar kawance ce a fannin hadin gwiwa da kasarsa, kuma ta taka rawar gani wajen bunkasa ci gaban kasar dake yammacin Afirka.
Shugaba Embalo, ya yi tsokacin ne yayin zantawarsa da manema labarai a filin jiragen sama na Bissau, gabanin tasowarsa zuwa nan kasar Sin inda zai gudanar da ziyarar aiki. Ya ce, “Kasashen biyu su kasance kawaye na gargajiya tun farkon gwagwarmayar ’yantar da Guinea-Bissau.” (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp