Majalisar ƙasa na shirin tura dokar hukumar raya Arewa maso Yamma (NWDC) ga Shugaba Bola Tinubu don sa hannu. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, wanda ya ɗauki nauyin ƙudirin, ya nuna kyakkyawan fatan cewa Shugaban zai sanya hannu a dokar. Dukkan ɓangarorin biyu na Majalisar Dokoki sun riga sun sahale dokar, wadda ke da nufin magance matsalolin da yankin Arewa maso Yamma ke fuskanta.
Sanata Barau ya jaddada cewa wucewar dokar ya dace da jajircewar Shugaba Tinubu na canza ƙasar da dawo da ita kan hanyar ci gaba da bunƙasa. NWDC ana sa ran za ta magance matsaloli a jihohi bakwai na Arewa maso Yamma—Kano, da Kaduna, da Katsina, da Kebbi, da Jigawa, da Sokoto, da kuma Zamfara.
Ana sa ran hukumar za ta farfado da ababen more rayuwa da ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga suka lalata, ta yadda za ta taimaka wajen ci gaban yankin da ake take da mai samar da abinci ga ƙasa baki ɗaya.
A cikin jawabin sa, Sanata Barau ya gode wa Shugaban Majalisar Dattawa, da Kakakin Majalisar Wakilai, da abokan aikin sa saboda goyon bayan da suka bayar kan dokar.
Ya jaddada muhimmancin hukumar wajen magance matsalolin yankin da na ƙasa baki ɗaya kuma ya nuna yaƙininsa kan jajircewar Shugaba Tinubu wajen canza ƙasar kamar yadda aka shimfida a cikin ƙudirorin gwamnatin Bola Tinubu.