Jiya Talata, an baiwa masanin kimiyya da fasaha na kasar Sin Li Di, lambar yabo ta Marcel Grossmann, bayan da masanin ya jagoranci aikin kera babban madubin hangen nesa mai fadin mita 500 mallakin kasar Sin wato FAST. Kaza lika, Li Di shi ne masanin kimiyya da fasahar kasar Sin na farko da ya samu wannan lambar yabo, bisa sakamakon kimiyya da fasaha da ya samu a kasar Sin.
An gudanar da taron gabatar da lambar karramawa na Marcel Grossmann ne tsakanin ranekun 7 zuwa 12 ga watan Yulin nan a birnin Pescara dake gabashin kasar Italiya. Kuma a jiya Talata aka bayar da lambar yabo ta Marcel Grossmann ga Li Di, bisa muhimmiyar rawar da ya taka wajen jagorantar aikin kera Babban Madubin FAST, wanda ya ba da taimako wajen auna karfin maganadisun sararin samaniya.
- Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Ya Yi Sabbin Naɗe-Naɗe 8
- An Kaddamar Da Dandalin Tattaunawa Na Nishan Kan Wayewar Kan Duniya A Lardin Shandong Na Kasar Sin
Babban Madubin FAST wanda aka fi sani da “Idon duba sararin samaniya na kasar Sin”, yana gundumar Pingtang dake lardin Guizhou, shi ne kuma babban madubin hangen nesa mai harba lantarki mafi fadi a dukkanin fadin duniya.
Lambar yabo ta Marcel Grossmann, ita ce lambar karramawa mafi muhimmanci a fannin ilmin aikin kira a duniya, an kuma kaddamar da ita ne tun a shekarar 1985. (Mai Fassara: Maryam Yang)