Sakamakon jerin matakan da kasar Sin ta gabatar a baya bayan nan na samar da sauki ga baki da ke zuwa kasar Sin, ciki har da shiga kasar ba tare da biza ba da saukaka wa baki hanyoyin biyan kudi da sauransu, baki da ke zuwa nan kasar don yawon shakatawa na karuwa da gaske, wadanda kuma suka harhada hoton bidiyo na Vlog bisa abubuwan da suka gani da ido, kuma suka watsa ta kafofin sada zumunta. A bidiyoyin da suka dauka, ana iya ganin biranen kasar Sin cikin yanayi mai ni’ima da ma nau’o’in abinci masu dadi, baya ga jirgin kasa mai saurin gaske da motoci marasa matuka da makamantansu, da suka shaida ci gaban al’ummar kasar Sin.
Duk da bambancin launin fatansu da harsunansu da mahangarsu, amma wadannan baki kusan ra’ayinsu ya zo daya bayan ziyararsu a kasar Sin, wato kasar Sin da suka gani da ido ta sha bamban kwarai da yadda suka zata kafin zuwansu nan kasar. Da yawa daga cikin bakin sun ce, sun sha jin labarai marasa kyau daga bakin ‘yan siyasa da kafofin yada labarai na kasashen yamma, don haka, sun damu sosai kafin su tashi zuwa nan kasar, sai dai bayan isowarsu, sun tarar da cewa, akwai tsaro da saukin rayuwa da ma al’umma masu zafin nama a nan kasar.
- Xi Jinping Ya Yi Shawarwari Tare Da Takwaransa Na Kasar Guinea Bissau
- An Kaddamar Da Dandalin Tattaunawa Na Nishan Kan Wayewar Kan Duniya A Lardin Shandong Na Kasar Sin
A sa’i daya kuma, shirye-shiryen bidiyon da wadannan baki masu yawon shakatawa suka watsa masu lakabin“ChinaTravel” sun samu matukar farin jini ta shafukan kafofin sada zumunta na kasa da kasa, har ma“ChinaTravel” tamkar ya zamanto sirrin yadda wani bidiyo ke iya samun karbuwa. Abin lura shi ne, dimbin ra’ayoyin da masu bibbiyar shafukan suka bayyana sun wuce irin ra’ayoyin da a kan bayyana game da shirye-shiryen yawon shakatawa, inda suka soki kafofin yada labarai na kasashen yamma bisa yadda suka gurbata gaskiya, sun kuma yaba wa masu harhada wadannan shirye-shiryen bidiyo bisa yadda suka taimaka wajen fahimtar da karin al’umma gaskiyar lamarin. Wasu masu bibbiyar shafukan sun kuma bayyana niyyar zuwa kasar Sin don su gani da idonsu. Baya ga haka, wasu baki da suka taba zuwa kasar Sin ko kuma suka shafe wasu lokuta suna rayuwa a kasar sun bayyana ra’ayoyinsu cewa, “Da ba ka ga abubuwa da ido a kasar Sin ba, da ba ka san yadda kafofin yada labarai na kasashen yamma suka kasance abin dariya ba.”
Amma me ya sa wadannan shirye-shiryen bidiyon suka samu matukar karbuwa a shafukan sada zumunta? To dalili shi ne yadda wadannan baki da suka yi yawon shakatawa a kasar Sin suka gyara fahimtar al’umma game da kasar Sin, bisa abubuwan da suka gani da ido a kasar. Wasu baki sun ce, a baya ba su samu cikakkiyyar fahimtar kasar Sin ba, kusan ba su iya koyon kome ba game da kasar Sin a makaranta, kuma bayanan da suka samu daga kafofin yada labarai da ‘yan siyasa shi ne “kasar Sin na da koma baya, kasa ce mai hadari, kuma kasa ce mai sharri.” Amma da suka zo nan kasar, sun tarar da cewa, sam sam kasar ba haka ba ce.
Dalilin da ya sa “ChinaTravel” ke matukar samun karbuwa shi ne sabo da irin al’adun kasar mai dadadden tarihi da ma yadda al’ummar kasar ke karbar baki da hannu biyu-biyu, haka kuma sabo da irin niyyar kasar Sin ta dada bude kofarta ga duniya. Muna fatan karin aminanmu ‘yan Afirka za su samu damar zuwa kasar Sin, sabo da kamar yadda Bahaushe kan ce, gani ya kori ji, da zuwanku nan za ku iya fahimtar hakikanin yanayin da ake ciki a kasar.
Kasar Sin na muku lale marhabi.