Alkaliyar Babbar Kotun Jihar Kebbi ta biyu, Mai shari’a Nusurat Ibrahim, ta sanya ranar 24 ga Yuli, 2024, ga CSP Abdullahi Bala Rano da ya gabatar da shaidu don kare kansa kan zargin karya yarjejeniyar kasuwanci.
Wani dan kasuwa mai suna Bashar Ibrahim da wasu mutane hudu ne suka maka CSP Abdullahi Bala Rano a gaban kotu inda suka nemi Kotun da ta tilastawa wanda ake kara ya biya kudaden kamar yadda yarjejeniyar kasuwancinsu ta tanada.
- Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli Ta Ba Ƙananan Hukumomi ‘Yancin Cin Gashin Kansu
- Sheikh Daurawa Ya Yi Kira Ga Musulmi Da Su Nisanci Zanga-zanga Kan Adawa Da Tsadar Rayuwa
A cikin takardar karar, masu karar sun sanar da Kotu cewa, akwai dangantaka ta Kasuwanci a tsakaninsu da wanda suke kara, bayan sun amince da gudanar da Kasuwancin Manja inda suka zuba jari a hannun CSP Abdullahi Bala Rano da ke aiki da rundunar ‘yansanda ta jihar Kebbi.
A zaman kotun da ke Birnin Kebbi, Mai shari’a Nusurat Ibrahim, ta umurci wanda ake kara ta hannun Lauyansa da ya bayyana kariyarsa/shaidunsa kan tuhumar da ake masa zuwa ranar 24 ga watan Yuli.
Lauyar masu shigar da kara, Barista Munirat O.Yahaya wacce ta jagoranci shaidu uku na karshe don ba da babbar shaida, ta ce a bangaren masu kara sun rufe kararsu bayan gabatar da shaidu Mutum shida.