A yau ne a yayin babban taro karo na biyu na dandalin tattaunawar ayyukan more damammakin ci gaban duniya na bai daya, aka bude cibiyar nuna hadin gwiwar Sin, Afrika (Habasha) da kungiyar raya masana’antu ta MDD a nan birnin Beijing.
An bayyana cewa cibiyar ta nune-nune ita ce aikin nune-nune na farko da hukumar kula da hadin gwiwar kasa da kasa kan harkokin ci gaba ta kasar Sin ta sa kaimin bangarorin uku suka aiwatar tare bisa tsarin shawarar raya kasa da kasa. Ta hanyar hadin kai tsakanin bangarori daban-daban, da sa hannun bangarori daban daban, da samar da dandalin mu’amala daban-daban, cibiyar tana tallafawa bunkasuwar masana’antu da zamanintar da aikin gona da horar da kwararru a Afirka. (Yahaya)