Assalamualikum masu karatu barkanmu da sake haduwa cikin wannan mako cikin shirin namu mai Albarka Girki Adon mace. Yau mun kawo muku tsarabar yadda ake Lemun Kwakwa da Abarba.
Da farko dai ga abubuwan da za ki tanada; Kwakwa, Abarba, Ruwa da Sukari.
Wannan hadin yana bukatar abin markade ( blender).
Da farko dai za ki wanke kwakwarki da Abarba, sai ki yanka su daidai yadda ba zai baki wahala ba, sai ki dauko abin markade ki zuba kwakwarki da Abarba tare, sai ki zuba ruwa sosai yadda zai markadu cikin sauki. Bayan nan za ki dauko abin tata ki tace, sai ki zuba shi cikin wani abin da za ki kara masa Sukari daidai yadda kike so sai ki kara da kankara don ya yi sanyi. Lemun kwakwa da abarbarki ya yi. Asha lafia