Wata kotu a Kenya ta umarci bayar da diyyar tsabar kudi har Dala miliyan 78 ga matar dan jaridar nan dan Pakistan da ‘yansandan kasar suka harbe a wani shinge kimanin shekaru biyu da suka gabata.
Arshad Sharif dai mai gabatar da shirye-shirye ne a gidan talbijin kuma ya yi suna kan sukar sojin Pakistan kan rashawa da cin hanci a kasar.
- Shugaban Kenya Ya Kori Ministocin Kasar Baki Daya Daga Aiki
- Sauya Fasalin Dimokuradiyyar Afirka: Lokaci Ya Yi Da Za Mu Yada Kwallon Mangwaro Mu Huta Da Kuda
Danjaridar wanda ya rasu ya bar ‘ya’ya biyar ya sha samun barazanar kisa kuma ya sanar da babban alkalin Pakistan, kafin ya tsere ya bar kasarsa zuwa wata kasar domin neman mafaka.
Kisan Sharif dai da ‘yansandan na Kenya suka yi a garin Kajiado ya tayar da hankalin al’umma sannan kuma jan kafar da jami’ai suka yi kan batun ya janyo suka daga jami’an Majalisar Dinkin Duniya inda suka soki hukumomin Kenya da na Pakistan.