• English
  • Business News
Saturday, August 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NAHCON Ta Kafa Kwamitin Karbar Korafe-korafe

by Sulaiman and Bello Hamza
1 year ago
in Labarai
0
Nahcon
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Domin kara inganta ayyyukan ta, Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya NAHCON ta kafa kwamiti domin karbar korafa-korarfe daga wadanda suka yi aikin Hajjin bana da kuma wadanda suka gudanar da aiki Umara kuma suna da wani korafi a kan hukumar ko kuma wani ma’aikaci ko kuma bangaren masu ayyuka a karkashin hukumar, dasu gabatar da korafinsu ga hukumar domin daukar matakin gyara a yayin aikin hajjin shekara mai zuwa.

Bayanin haka ya fito ne a takardar sanarwa da hukumar ta buga a wasu jaridun kasar nan, hakan kuma ya biyo bayan wasu korafe-korafe ne wasu masu ruwa da tsaki suka gabatar a kafafen sadarwa na intanet ciki har da Gwmanan Jihar Neja Muhammad Bago, inda ya nemi a rusa hukumar a dawo da harkokin aikin hajji ga jihohi.

  • Zai Yi Wahala A Magance Matsalar Tsaro Matukar… – Janar Lagbaja
  • Peng Liyuan Ta Yi Kira Da Karin Hadin Gwiwa Tsakanin Kasa Da Kasa Domin Takaita Cututtukan Kanjamau Da Tarin Fuka

Sanarwa ta bayar da wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Agusta 2024 ga duk duk wanda yake da wani tsokaci ko shawarwari na yadda za a kara inganta aikin Hajji da Umara a shekara mai zuwa ya gabatar wa hukumar.

An kuma bukaci duk mai korafi ya rubuta cikakken sunansa da adireshinsa ya kuma aika zuwa hedikwatar hukumar da ke Abuja.

A wani bangaren kuma Hukumar Koli ta Addinin Musulunci (NSCIA) ta bayyana aniyyarta na bincikar Hukumar Aikin ta Nijeriya NAHCON a kan yadda ta gudanar da aikin hajjin bana musamman ganin yadda aka samu korarfe-korafe daga bangarori da dama, musamman daga masu ruwa da tsaki inda suka nuna rasahin gamsuwarsu a kan yadda aka gudanar da wasu lamurrori da suka shafi aikin hajjin bana.

Labarai Masu Nasaba

Gwamna Sani Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Kashe Wani Matashi A Barnawa

Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

Hukumar ta bayyana wannan shiri nata ne bayan taron da ta gabatar na kwamitin zartarwarta da aka yi a babban dakin taron babban masallacin kasa da ke Abuja ranar Asabar 6 ga watan Yuli 2024.

A takaradar bayan taron da babban sakatarenta, Farfesa Isahak Oloyede ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa, a halin yanzu hukumar na jiran rahoton yadda aka gudanar da aikin hajjin ne daga NAHCON kafin ta fara gudanar da nata binciken da bin diddigin korarfe-korafen da masu ryuwa da tsaki suka gabatar a kan yadda aka gudanar da aikin hajjin bana.

Hukumar wadda ita ce, a kan gaba a cikin kungiyoyin addinin musulunci a Nijeriya ta kara da cewa, “Ganin korafe-korafe daga masu ruwa  da tsaki a kan yadda aka gudanar da harkokin da suka shafi aikin hajjin bana, taron ya yanke shawarar a jira fitiowar rahoton NAHCON a kan yadda ta jagoranci aikin hajin bana kafin a fara aikin binciken, an kuma amince da kiran babban taro na kasa domin tattauna lamarin aikin hajjin gaba daya. An kuma nuna bukatar a samar da hanyar tattaunawa a tsakanin gwanmati, NAHCON da kuma kungiyar NSCIA domin samun fahimtar juna a dukkan matakan aikin hajji, ta haka ne al’ummar musulmi musamman alhazai za su amfana da irin gudummawar da gwamnati ke bayarwa a duk shekara a kan aikin hajji.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Hajjin BanaNAHCON
ShareTweetSendShare
Previous Post

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Samu Sakamako Mai Kyau A Rabin Farko Na Shekarar Bana

Next Post

Ƴan Jarida Biyu da Aka Sace a Kaduna Sun Shaƙi Iskar Ƴanci

Related

Gwamna Sani Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Kashe Wani Matashi A Barnawa
Labarai

Gwamna Sani Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Kashe Wani Matashi A Barnawa

7 hours ago
Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya
Rahotonni

Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

7 hours ago
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP
Labarai

Babu Dalilin Da Zai Sa ‘Yan Nijeriya Su Yi Talauci – Tinubu

8 hours ago
Akwai Bukatar Samar Da Sauyin Zaman Lafiya Mai Dorewa A Duniya — Maryam Bukar
Labarai

Akwai Bukatar Samar Da Sauyin Zaman Lafiya Mai Dorewa A Duniya — Maryam Bukar

10 hours ago
UBEC Ta Kaddamar Da Makarantun Zamani 21 A Sassan Nijeriya
Labarai

UBEC Ta Kaddamar Da Makarantun Zamani 21 A Sassan Nijeriya

11 hours ago
Gwamnatin Katsina Za Ta Samu Kudaden Bunkasa Ilimi
Labarai

Tetfund Ta Samar Da Naira Biliyan 100 Don Inganta Ilimin Likitanci – Masari

12 hours ago
Next Post
Ƴan Jarida Biyu da Aka Sace a Kaduna Sun Shaƙi Iskar Ƴanci

Ƴan Jarida Biyu da Aka Sace a Kaduna Sun Shaƙi Iskar Ƴanci

LABARAI MASU NASABA

Wang Yi: Ya Kamata A Mutunta Tarihi Domin Magance Sake Yin Kuskure

Wang Yi: Ya Kamata A Mutunta Tarihi Domin Magance Sake Yin Kuskure

August 15, 2025
An Samu Rarrabuwar Kawuna A Jam’iyyar ADC Kan Shugabancin David Mark

An Samu Rarrabuwar Kawuna A Jam’iyyar ADC Kan Shugabancin David Mark

August 15, 2025
Ya Kamata A Yi Wa Japan Jinyar Cutar “Mantuwar Tarihi”

Ya Kamata A Yi Wa Japan Jinyar Cutar “Mantuwar Tarihi”

August 15, 2025
Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa

Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa

August 15, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Bikin Mu’amalar Al’adu Da Jama’a A Hedkwatar MDD

CMG Ya Kaddamar Da Bikin Mu’amalar Al’adu Da Jama’a A Hedkwatar MDD

August 15, 2025
Gwamna Sani Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Kashe Wani Matashi A Barnawa

Gwamna Sani Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Kashe Wani Matashi A Barnawa

August 15, 2025
Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

August 15, 2025
Gasar Wasannin Mutum Mutumin Inji Ta Duniya Ta 2025 Na Gabatar Da Sabbin Fasahohin Zamani

Gasar Wasannin Mutum Mutumin Inji Ta Duniya Ta 2025 Na Gabatar Da Sabbin Fasahohin Zamani

August 15, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Babu Dalilin Da Zai Sa ‘Yan Nijeriya Su Yi Talauci – Tinubu

August 15, 2025
Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Yadda Ya Kamata A Watan Yuli

Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Yadda Ya Kamata A Watan Yuli

August 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.