Da yammacin ranar 10 ga watan Yuli, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Guinea-Bissau Umaro Mokhtar Sissoco Embalo, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin. A yayin tattaunawar, shugabannin kasashen biyu sun amince da inganta huldar dake tsakanin Sin da Guinea-Bissau, zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare. Shugaba Embalo ya bayyana a wata hira da dan jaridan babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) a kwanan baya cewa, inganta wannan alaka na da matukar muhimmanci.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a duniya. A cewarsa, “A ko da yaushe kasar Sin tana goyon bayan matsayin kasar Guinea-Bissau a MDD, a duk lokacin da muke bukatar goyon bayan kasar Sin, Sin tana goyon bayanmu ba tare da wata tangarda ba. Muna kuma goyon bayan kasar Sin har kullum.”
- Ya Zama Wajibi Amurka Ta Sauke Nauyin Dake Wuyan Ta Game Da Kasar Afghanistan
- Wurin Da Ya Fi Ba Ni Wahala A Daukar Shirin Labarina – Hadiza Abubakar
Yayin da yake magana kan tasirin hadin kai tsakanin Sin da Afirka ga kasashe masu tasowa da ma duniya baki daya, Embalo ya ce, a cikin kasashen Afirka 54, babu wadda ba ta samu nasara sakamakon kokarin kasar Sin ba. Har ila yau, ya ce Sin ce kasar da ta fi yawan ofisoshin jakadanci a Afirka, hakan ya nuna muhimmancin da take baiwa nahiyar. (Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp