Gidauniyar Tunawa da Ahmadu Bello Sardauna da ke Kaduna ta kadu matuka bisa yadda wani gini a garin Jos da ke jihar Filato ya fado kan daliban makarantar Saint Academy da ke tsaka da daukar darasi.
A wata sanarwa da gidauniyar ta rabawa manema labarai a Kaduna Mai dauke da Sanya Hannun Darakta Janar na gidauniyar, Injiniya Abubakar Gambo Umar, ya bayyana lamarin a matsayin wani rashi ga al’ummar kasa baki daya.
- Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Samu Sakamako Mai Kyau A Rabin Farko Na Shekarar Bana
- Ba Zan Taba Mantawa Da Zamowata Gwarzuwar Banki Sau Biyu A Jere Ba – Fatima Gana
Yace ” Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga Gwamnatin Jihar Filato, Al’umma da kuma iyayen wadanda iftila’in ya rutsa da su, wannan babban rashin da aka yi a ranar Juma’a Wanda akwai bukatar a dauki matakan da suka dace wajen kare afkuwar irin wannan lamarin nan gaba”
Shugaban ya bukaci gwamnati da ta tabbatar da cewa ta dauki nauyin duk wani nauyin kula da wadanda iftila’in ya rutsa a asibiti da kuma daukar matakan da suka dace na hana afkuwar hakan a nan gaba.
Akan Hakan, gidauniyar ta bayyana gamsuwarta bisa matakan gaggawa da aka dauka na kai gudunmawa wurin da iftila’in ya faru, inda ya yi adduar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu yayin ruftawar Ginin inda yace ya zama wajibi idan za’a sake Gina makarantar a yi mai inganci da nagarta