A babban filin wasa na Olympia stadion mai daukar dimbin yan kallo fiye da 74,000 da ke birnin Berlin, zai amshi bakuncin wasan karshe na gasar kofin kasashen Turai na EURO tsakanin kasashen Ingila da Spain da misalin karfe 8 na daren yau, Lahadi agogon Nijeriya.
A wannan rana ta Lahadi ne kyaftin din tawagar kwallon kafa ta kasar Ingila Harry Kane ke fatan ganin ya lashe kofi na farko a tarihin rayuwarsa ta kwallon kafa a Berlin.
- Kamfanin Jiragen Ruwa Na Maersk Zai Zuba Jarin Dala Miliyan 600 A Nijeriya
- Saudiya Za Ta Kafa Masana’antun Kera Kayan Aikin Gona A Nijeriya
A bangare daya kuwa, matasan yan wasan kasar Sifaniya Lamine Yamal da abokin kwallonsa Williams Nico ke fatan ganin sun jagoranci kasar domin lashe wannan kofi na EURO, wanda zai sa su kafa tarihi a kwallon kafa wanda za a dade ba a manta dashi ba.
Kasashen biyu sun hadu da juna sau 27 a mabanbantan lokuta a tarihi, inda kasar Ingila take kan gaba wajen samun nasara wanda ta yi har sau 13 inda aka yi canjaras 4 sai kuma Sipaniya da ta samu nasara a wasanni 10 da suka buga a tsakaninsu.