Sufeto-Janar na ‘yansandan Nijeriya, Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin dakatar da tilasta fara aiwatar da rajistar motoci na e-Central Motor Registry (e-CMR) da aka shirya daga ranar 29 ga watan Yuli.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa inda ya ce an dakatar da shirin tilasta dokar ne domin bai wa jama’a damar wayar da kan jama’a da fahimtar da su kan tsari da fa’ida da ingancin rajistar e-CMR din
- Ganduje Da Mai Dakinsa Za Su Gurfana A Gaban Kotu A Kano
- Napoli Ta Nada Antonio Conte A Matsayin Sabon Kocinta
A cewarsa duk jami’an da aka samu suna zamba ko cin zarafin jama’a da sunan ba su da takardar shedar e-CMR, din rundunar za a hukunta su, inda ya bukaci jami’an ‘yansanda da su daina neman takardar shaidar e-CMR, yana mai cewa za a aiwatar da dokar ne da musamman wanda za a ranar da su ranar daga baya.
Adejobi, ya ce an fito da rajistar amfani da e-CMR ne domin magance kalubalen laifukan da suka shafi abaɓen hawa da kuma kare hakin jama’a da na kamfanoni da kuma na’urar tantancewa ta ‘yansanda domin inganci da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijeriya baki daya.
Dalilin haka kakakin rundunar ‘yansandan ya yi kira da a samu fahimta da goyon bayan ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa da su yi rajistar tsarin e-CMR din.