Kungiyar Fityanul Islam ta nesanta kanta game da shirin zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa a fadin Nijeriya wacce aka shirya gudanarwa daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Augusta a fadin kasar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, ustaz Sani ibn Salihu wacce shugabanta Sheikh Dakta Muhammad Arabi AbulFathi ya sanya wa hannu a ranar 15 ga watan Yuli, 2024.
- Hargitsi Ya Ɓarke A Majalisar Dokokin Kano Kan Muƙamin Ganduje
- Sabuwar Shekarar Musulunci: Fityanul Islam Ta Zaburar Da Musulmi Kan Bin Addini
Kungiyar ta yi nuni da cewa, irin wannan gagarumin mataki da ake shirin dauka bai cika haifar wa al’umma alheri ba.
“Kungiyar Fityanul Islam ta Nijeriya ta nesanta kanta da irin wannan gagarumin mataki na zanga-zanga domin za a iya samun marasa kishin kasa su tayar da tarzoma da ka iya haifar da rugujewar bin doka da oda.
“Don haka, kungiyar Fityanul Islam ta Nijeria tana kira ga daukacin al’ummar musulmin kasar da su gujewa irin wannan zanga-zangar, maimakon haka, musulmi su yi azumi da addu’o’in neman taimakon Allah a dukkan masallatanmu.Mu yi saukar Al-Qur’ani mai girma sau miliyan cikin kwanaki goma da kuma tsunduma cikin Istighfar marasa adadi (Neman Gafarar Allah) don magance kalubalenmu.” In ji Ustaz Sani
Sanarwar ta kuma yi kira ga gwamnati da ta sake bitar duk wasu tsare-tsare, musamman wadanda suka jefa ‘yan Nijeriya cikin mawuyaciyar rayuwa.
“Muna Addu’ar Allah ya kawo wa kasar mu mafita ya kawar da kalubalan da suka dabaibayeta”