Gwamnatin Jihar Kano ta gabatar da sabbin tuhume-tuhume kan tsohon gwamnan jihar kuma Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Kwamishinan Shari’a na jihar, Musa Lawan.Â
An zarge su da karkatar da Naira miliyan 240.
Har wa yau an zarge su da hada kai wajen aikata laifi da karkatar da dukiyar gwamnati, wanda hakan ya saba da sashe na 308 da 309 na kundin laifuka.
- Southgate Ya Ajiye Aikin Horas Da Ingila
- Matsalar Karancin Abinci Za Ta Ƙare Nan Ba Da Jimawa Ba – Gwamnatin Tarayya
A sabuwar tuhumar an ce sun karkatar da kudaden don amfanin kashin kansu, wanda hakan ya haifar wa gwamnatin Jihar Kano asara.
Masu gabatar da kara suna shirin gabatar da shaidu guda hudu, kan zargin cewa Ganduje da Lawan sun yi amfani da mukamansu wajen karkatar da kudaden don shari’ar ma’aikatan Jihar Kano da hukumar EFCC ke gudanarwa.
An ce kudaden an yi amfani da su wajen hana EFCC binciken zargin cin hanci da rashawar da ta ke yi wa Ganduje.
Kotun ba ta sanya ranar da za a fara sauraren shari’ar ba.
Wannan shari’ar ta shiga jerin shari’ar da Ganduje ke fuskanta a jihar.
Idan ba a manta ba, Ganduje da matarsa, da wasu na fuskantar tuhume-tuhume da suka hada da cin hanci da karkatar da kudaden jama’ar jihar.
An dage sauraron shari’ar har zuwa watan Oktoba don ci gaba da shari’ar, duk da cewa kotun ta ki amincewa da neman kama wadanda ake tuhuma.