Yau Talata, ma’aikatar kula da masana’antu da fasahohin bayanai ta kasar Sin ta fitar da sabbin alkaluma na masana’antar kera jiragen ruwa a farko rabin shekarar bana, wadanda suka nuna cewa, masana’antar na ci gaba da samun karuwar tagomashi, kuma tana kan gaba a duniya.
Bisa alkaluman, a farkon rabin shekarar bana, manyan alamomi guda uku na kasar Sin da suka hada da kammala aikin kera jiragen ruwa, da sabbin oda, da odan da ba a kammala ba, sun kai kashi 55 cikin dari, da kashi 74.7 cikin dari, da kuma kashi 58.9 cikin dari bisa na kasuwar duk duniya baki daya.
Yawan kudaden da kasar Sin ta samu daga fitar da jiragen ruwa zuwa waje na ci gaba da karuwa, kuma sama da kashi 70 cikin dari na duk sabbin odar kera jiragen ruwa guda 10 a duniya na zuwa hannun kamfanonin kera jiragen ruwa na kasar Sin. (Safiyah Ma)