A karon farko, an samu gagarumar nasara a Jihar Gombe, wajen samun raguwar rikicin manoma da makiya a shekarar 2023.
A shekarun baya da suka gabata, an fuskanci rikicinn manoma da makiya da dama, wanda hakan ya jawo rasa rayuka tare da kawo nakasu a harkokin tattalin arzikin jihar.
Sai dai, a kokarin kawo karshen irin wadannan rikice-rikice a tsakanin manoman da makiya, a shekarar 2020; gwamnatin jihar ta sake farfado da wani kwamiti, domin dakile sake afkuwar rikicin a tsakaninsu.
- Ƴansandan Gombe Sun Yi Ram Da Ɓarayin Hanyar Jirgin Ƙasa
- Ko Kun San Miliyan Nawa Gombe Ke Kashewa Don Tsaftace Jihar A Duk Wata?
An dai dora wa wannan kwamiti nauyin alhakin yin dukkannin mai yiwuwa, don kawo karshen rikicin a tsakanin manoman da kuma makiyayan.
Bugu da kari, kwamitin ya kuma gudanar da tarurruka da dama ta hanyar aiwatar da taro, domin jin ra’ayoyin mutane, musamman a tsakanin masu ruwa da tsaki; don kawo karshen dukkannin wani nau’i na tashin-tashina a tsakaninsu.
Ko a makon da ya gabata, an kira shugabannin dukkanin bangarorin manoman da makiyayan, domin gudanar da taron jin ra’ayoyin al’umma a jihar ta Gomben, musamman don daidaita al’amuran.
A jawabinsa a wajen taron, Kwamishinan Ma’aikatar Aikin Noma da Kula da Kiwon Dabbobi na Jihar, Dakta Barnabas Malle ya bayyana fatan cewa, ba za a sake samun wani rikici a tsakanin manoma da makiyaya a jihar ba, musamman duba da cewa; gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen kawo karshen duk wani rikici a tsakanin manoma da makiyayan a jihar