Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dakta Suleiman Umar a matsayin shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna (KADPOLY).
Nadin wanda ya fara aiki nan take tun daga ranar 27 ga watan Yunin 2022 kuma zai shafe tsawon shekara biyar a wa’adin farko.
- Rashin Tsaro: Ba Wani Abun Mamaki Idan ‘Yan Bindiga Suka Sace Buhari – Buba Galadima
- An Bude Taron Dandalin Kare Hakkin Dan Adam Na Beijing Na Shekarar 2022
Wannan bayanin na kunshe ne ya cikin wata sanarwar da mataimakin rajistara kuma mai kula da sashen yada labarai Samuel Y. Obochi, ya fitar a ranar Talata tare da bai wa majiyarmu kwafin sanarwar.
Dakta Suleiman Umar ya fito daga karamar hukumar Kaduna ta Kudu a jihar.
Ya samu shaidar digirin digirgir a sashen ilimin lissafi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Shi din kuma kwararren mambar kungiyar masana a fannin lissafin ne wato (MAN).
Ya yi aiki sassa daban-daban a Kwalejin ciki har da zama shugaban tsangaya da mataimakin shugaba a sashen gudanar da mulki.
Kafin masa wannan nadin, Dakta Suleiman shi ne ke rikon mukamin shugaban Kwalejin.