A ranar 21 ga wata, an fitar da cikakken bayanin ‘Kudurin kwamitin kolin JKS kan zurfafa gyare-gyare da sa kaimi ga zamanantarwa irin ta kasar Sin” da cikakken zama na uku na kwamitin kolin JKS karo na 20 ya yi nazari tare da amincewa da shi, a cikin kudurin, an gabatar da shiri na musamman kan batun bude kofa ga kasashen waje. Manazarta na ganin cewa, hakan na dauke da wata alamar da ta nuna cewa, kasar Sin za ta fadada bude kofarta ga kasashen waje, kuma sauye-sauyen da kasar ke yi zai samar da karin moriyar bude kofa ga kasashen duniya.
Abin da kasar Sin ke rabawa duniya da farko, shi ne babbar kasuwa mai girman gaske. Kuma abu mafi mahimmanci shi ne, bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin na ci gaba daga tsarin bude kofa bisa matakan samar da hajoji zuwa bude kofa a matakin hukumomi kamar yin kwaskwarima ga dokoki, ka’idoji, da gudanarwa da bukatu. Kasar Sin ta tabbatar wa duniya a zahiri cewa, abin da take nema ba zamanantar da kanta kadai ba ne, sai zamanantar da duniya tare da samun ci gaba cikin lumana, da hadin gwiwar moriyar juna, da samun wadata tare. (Mai fassara: Yahaya)