Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti na musamman domin gudanar da bincike kan mutanen da ke yi wa harkar man fetur da iskar gas zagon kasa da zummar ganin an dauki mataki a kansu.
Wannan ya biyo bayan zargin da Aliko Dangote ya yi cewar wasu mutane na yi wa matatarsa zagon kasa wajen ganin Nijeriya ba ta ci gajiyar aikin da ta ke yi ba.
- Da’awar Zanga-zanga: An Sako Abusalma Daga Gidan Yari
- Yarjejeniyar Beijing: Mabudin Zaman Lafiya A Zirin Gaza
Shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya bukaci ‘yan kwamitin da su yi aiki tukuru wajen gano irin wadannan mutane da suka dade suna hana Nijeriya ci gaba a wannan bangare na tattalin arzikin kasa.
Takaddama ta yi zafi tsakanin Dangote da kamfanin NNPC dangane da samar wa matatarsa man da yake bukata domin gudanar da aikinsa, yayin da bangarorin biyu ke zargin juna da saba ka’idar aiki.
Sai dai an yi wani zama tsakanin Dangote da wakilan kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL don daidaita tsakanin bangarorin biyu.
Majalisar dattawa ta sha alwashin bankado masu yi wa Nijeriya zagon kasa a wannan bangare mai matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasa, musamman wajen wadata kasar da tacacen mai wanda ake kashe makudan kudaden kasashen waje domin saya.