Babban Sufeton ‘yansada na kasa, Kayode Egbetokun, ya ce sun shirya domin tunkarar zanga-zangar da matasan kasar nan ke shiryawa a watan Agusta.
Sai dai da yake magana bayan ganawa da manyan jami’an rundunar, Kayode Egbetokun ya yi kira ga matasa da hakura da zanga-zangar saboda gwamnati na kokarin duba korafe-korafensu.
- Da’awar Zanga-zanga: An Sako Abusalma Daga Gidan Yari
- Wang Yi: PLO Ita Ce Kadai Halatacciyar Wakiliyar Al’ummar Falasdinu
“Idan zanga-zangar ta lumana ce za ku ganmu muna kare masu zanga-zangar. Ba ma adawa da zanga-zangar lumana, za mu taimaka wa masu zanga-zangar lumana saboda ‘yancinsu ne” in ji shi.
“Amma kuma akwai alhaki a kanmu na kare rayuka da dukiyoyi. Ba za mu zauna muna kallon bata gari suna kona gine-gine da sunan zanga-zanga ba, ba za mu yarda da wannan ba.”
Yanzu haka dai matasa na ci gaba da yin gangami game da zanga-zangar a Intanet.